A cewar rahoton wakilin Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam Wal-Muslimin Sayyid Ali Akbar Ojagh-Nejad, shugaban Masallacin Jamkaran, a yayin taron tunawa da ranar bincike a Masallacin, ya yaba wa masu shirya taron inda ya bayyana cewa: "An gudanar da zama mai matukar amfani tare da halartar malamai da masana, kuma muna fatan wadannan tarurruka za su ci gaba akai-akai."
Yayin da yake nuni da kafa sakateriyoyi na musamman a fannin ilimin "Mahdawiyya" (al'amarin da ya shafi Imam Mahdi), ya kara da cewa: "Kafa saketariyar da kuma tsara ayyukan da za ta gudanar wani mataki ne mai muhimmanci da daraja, kuma Masallacin Jamkaran a shirye yake ya hada gwiwa da cibiyoyin ilimi domin sauke wannan nauyi yadda ya kamata."
Hujjatul Islam Wal-Muslimin Ojagh-Nejad, yayin da yake bayyana cewa a yau ana fuskantar kiyayya ce tsayayya kuma shiryayya, ya ce: "Akwai lokacin da gwagwarmaya ta takaita ga wasa takobi, amma a yau kayan fadan suna cikin aljihunmu; makiya sun shigo gidajenmu ta hanyar wayar hannu da duniyar yanar gizo. Wannan wata gaskiya ce da dukkanmu muka shaida da ita."
Shugaban Masallacin Jamkaran ya bada misali da yanayin rayuwar yau inda ya kara da cewa: "Yana yiwuwa yaronmu yana cikin dakinsa, amma ta fuskar tunani da kafofin watsa labarai yana can wani sashe na duniya. Wannan yana nuna cewa yanzu hanyoyin gargajiya na bada amsoshi (ga tambayoyin addini) ba zasu isa ba."
Hauzah/Shugaban Masallacin Jamkaran ya jaddada bukatar sabunta hanyoyin bayyana koyarwar addini ga sabbin tsatso, inda ya ce: "A yau, fagen gwagwarmayar al'adu ya tashi daga fada irin na gargajiya zuwa wayoyin hannu da duniyar gizo, kuma ba tare da sanin harshen matasa ba, isar da sakonni na akida ba zai yiwu ba."
Your Comment